An yi gudun famfalaki yayin da wata gawa tayi wuf! ta kamo hannu dan uwanta a Filato

An yi gudun famfalaki yayin da wata gawa tayi wuf! ta kamo hannu dan uwanta a Filato

-Wata gawa a jihar Filato ta kamo hannun wanda ke yi mata wanka

-Ance mamacin baya shiri da dan uwansa a lokacin dayake raye sakamakon rikicn kudin gado da suke yi

Jama’a sun shiga zullumi tare da fargaba a ranar Litinin 1 ga watan Mayu a asibitin kwararru na garin Jos a lokacin da gawar wani mamaci da ake shirin birnewa tayi wuf ta kamo hannun dan uwansa.

Wannan lamari mai cike da almara ya faru ne lokacin da gawar wani mutum mai suna Choji Zeng ta cafko hannun dan uwansa mai suna Gyang Zeng lokacin da yan uwansa suke yi masa wanka.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya shawarci gwamnati ta fara tatsan kowane mutum a Kano naira 1000

Ganin haka ya sa nan da nan sauran yan uwan da suke zagaye da gawar suka ranta ana kare, kowa na kiran kafa mai naci ban baki ba! Amma ma’aikatan aisibitin sun yi karfin hali, inda suka shigo suka raba gawar da dan uwan nata.

An yi gudun famfalaki yayin da wata gawa tayi wuf! ta kamo hannu dan uwanta a Filato
Akwatin gawa

Shima dan uwan mamacin, Gyang Zeng ya tabbatar ma maijiyar Legit.ng faruwar lamarin, yace ya kammala wanke gawar dan uwan nasa, yana cikin sanya masa likafani kenan, sai ya cafko masa hannu, yace nan fa ya sa ihu, yana neman agaji, har sai da ma’aikatan asibitin suka kwace shi.

Gyang yace “A lokacin daya rike min hannu, sai nace masa, haba Choju, so kake nima na bika ko kuwa me kake nufi ne”?

Daya daga cikin ma’aikatan asibitin yace sun saba ganin irin haka na faruwa a asibitin. Amma wani makwabcin mamacin, Mista Benjamin ya shaida ka kamfanin dillancin labaru, NAN, cewa

“ kafin rasuwan mamacin, sun samu rashin fahimta da kaninsa Zeng kan filayen gado, wata kila shiyasa ya kamo shi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wata mata tayi asaran yaronta ga yan kungiyar asiri

Asali: Legit.ng

Online view pixel