Ba mu halarci bikin auren 'yan luwadi a Zaria ba

Ba mu halarci bikin auren 'yan luwadi a Zaria ba

- Rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ta cafke mutane 53 ta kuma gurfanar da su a gaban kotu akan laifin halartar wani auren jinsi da aka shirya a garin Zaria

- Mutanen, wadanda aka kama ranar 15 ga watan Afrilu, sun musanta zargin da ake yi musu na hada baki, da yin taro ba bisa ka'ida ba

- Mai gabatar da kara Mannir Nasir ya ce laifukan sun saba wa sashi na 97, 100 da 197 (a) na dokar hana aikata laifuka

Rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ta cafke mutane 53 ta kuma gurfanar da su a gaban kotu akan laifin halartar wani auren jinsi da aka shirya a garin Zaria da ke jihar.

Mutanen, wadanda aka kama ranar 15 ga watan Afrilu, sun musanta zargin da ake yi musu na hada baki, da yin taro ba bisa ka'ida ba, da kasancewa mambobin haramtacciyar kungiya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya rawaito cewa mutanen sun gurfana ne a gaban kotun majistiri da ke unguwar Chediya a garin na Zariya.

Ba mu halarci bikin auren 'yan luwadi a Zaria ba
Rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ta cafke mutane 53 ta kuma gurfanar da su a gaban kotu akan laifin halartar wani auren jinsi

Mai gabatar da kara Mannir Nasir ya ce laifukan sun saba wa sashi na 97, 100 da 197 (a) na dokar hana aikata laifuka.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

Sai dai lauyan wadanda ake zargi Yunusa Umar ya ce yawancinsu dalibai ne kuma an tsare su ne ba bisa ka'ida ba, domin sun haura sa'o'i 24 a hannun hukuma.

Daga nan sai alkalin kotun ya bayar da belinsu, inda za a ci gaba da shari'a a ranar 8 ga watan Mayu.

An dai haramta luwadi da madugo a Najeriya, kuma ana matukar kyamar masu aikata hakan.

Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da ake tuhumar mutane da zargin aikata hakan ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon tsohon fasto da ya musulunta:

Asali: Legit.ng

Online view pixel